Daga cikin shugabanin Izala reshen Jos,Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid Gombe, yace akwai abun dubawa game da kiraye-kirayen a ware da wasu keyi inda ya bada misali da abinda ke faruwa a Sudan ta kudu.
Malamin wanda ke jihar Adamawa domin gudanar da wa’azin watan Azumi, yace dole ne kafofin yadda labarai su sake salo masamman ta fuskar fadan gaskiya da kuma kawo fahimtar juna ba wai tsayawa ana ance-kace ba.
Malamin ya kara da cewa, abinda ya kamaci Najeriya shine, a zauna a dunkule kasa daya kamar yada ake domin raba kasar ba zaiwa jama'ar kasar amfani ba.
Muhammad El-Yakub, babban darektan kafofin yada labarai na Gotel, yace kafofin yada labarai suma shugabanin al’umma da na addini dole ne a hada hannu domin tabbatar da cewa kasar ta zauna lafiya.
Yana mai cewa jama’ar daga bangarori dabam-dabam na kasar Najeriya, zasu fahimci cewa tafiyar da ake yi, ana yin sa ne bisa fahimtar juna kuma ba abinda yake haifarwa sai alheri. Da fatan bangarorin zasu fahimci haka.
Facebook Forum