Gwamnan ya bayyana haka a fadar gwammnatin jihar a wani sakon salla da ya gabatar wa al’ummar jihar .
Gwamnan yace an samu nasarori game da yakin da akeyi da kungiyar ta Boko Haram amma a ‘yan kwanakin nan an dan fuskanci matsaloli don haka akwai bukatar hada karfi da karfe na ganin cewa an kau dasu baki daya.
Yace ‘’ Ina son in mika godiya ta ga dukkan Al’ummar da suka taka rawa da kuma suka sadaukar da rayukan su wajen samar mana da zaman lafiya a wannan kasa domin a shekaru biyu da suka gabata muna cikin wani hali ne na kaka ni kayi, duk ko dacewa har yanzu muna cikin matsala, amma dole ne mu yaba wa shugaba Muhammadu Buhari da rundunar sojan kasar dama dukkanin jamian da suka basu tasu gudunmowar wajen yakar wadannan ‘yan taaddan’’,
Gwamnan yaci gaba cewa dole ne sai an kara kaimi kamar yadda yake cewa musammam ma a makonni biyu da suka gabata mun fuskanci matsaloli sosai kamar a garuruwa Damboa, Chibok, da Maiduguri, kai a kusan dukkan lungunar dake fadin wannan jihar.
Ga Haruna Dauda da Karin bayani
Facebook Forum