Kimanin mutane uku ne aka kashe a ciki harda dan Sanda daya an kuma kona ofishin ‘yan sandan dake garin Alawa, a yankin karamar hukumar Shiroro, ta jihar Nejan Najeriya.
Lamarin dai ya faru ne da yammaci jiya juma’a, bayanai sun nuna cewa ‘yan Sandan daga Minna sun je garin Alawa ne domin su kamo shugaban ‘yan banga na garin akan wata tuhuma da ake yimashi alamarin da ya haifar da wannan tashin hankali.
Hakimin Alawa, Alhaji Ibrahim Salihu, ya tabbatarwa muryar Amurka cewa matasan Alawa sun kashe dan Sanda daya da kuma kona ofishin ‘yan Sanda a garin na Alawa.
Itama rundunar ‘yan Sandan jihar Neja ta bakin kakakinta DSP, Bala Elkana, ta tabbatar da afkuwar lamari,yana mai cewa jami’an ‘yan Sandan sun je garin na Alawa, ne domin kamo shugaban ‘yan banga na garin saboda tuhumarsa da ake yi da hannu kan bacewar wasu mutane har su bakwai a yankin amma sai aka aukawa ‘yan Sandan.
Ya kara da cewa ‘yan bangan baya ga kashe dan Sanda da kuma kona ofishin ‘yan Sandan sun kwace daya daga cikin bindigogin ‘yan Sandan.
Kawo yanzu da kura ta lafa sai dai bayanai sun nuna cewa akwai zaman zulumi domin rashin sanin abinda zai iya biyo baya akan wannan lamari, a baya dai yankin na Alawa, ya sha fama da ‘yan fashin dake hallaka jama’a, da sace dabbobi da kuma yiwa mata fyade.
Facebook Forum