Rahotanni sun nuna cewa ana samun karuwan masu kallon Talabijin a kasashe masu tasowa, abinda aka sani da kasashe da suka cigaba.
A shekarar 1996, ne dai babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da wannan rana domin duba rawar da Talabijin ke takawa a rayuwar bil-Adama.
Dr Sulaiman Yar’adua, shugaban sashen koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero ta Kano, yace tasirin Talabijin ga dan Adam, shine yadda take mika sako ga jama’a da ake ji da kuma gani da ido, kasancewar akasarin mutane sun fi yarda da abinda suka gani idan aka kwatanta da wadda ji kawai.
Sai dai kasancewar Talabijin na tafiya da zamani ga kuma bukatar wutar lantarki,domin haka ake ganin cewa amfanin da Talabijin ko kuma dogaro dashi ba abune da ya zama wajibi ba a kasashe masu tasowa ganin yadda ake fama da karancin wutar lantarki.
Sai dai a cewar Dr Yar’adua, wannan lamari yakau domin kuwa yanzu akwai kafofi da dama na kallon Talabijin,domin ci gaban zamani akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajen isar da sako na Talabijin, misali ta wayar hannu ana iya kallon Talabijin.
Facebook Forum