Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

QATAR 2022: Morocco Ta Sabunta Tarihin Gasar Cin Kofin Duniya


Yan wasan kwallo Morocco
Yan wasan kwallo Morocco

Kungiyoyin Afirka sun yi ikirarin murkushe kungiyoyi da dama a gasar cin kofin duniya amma ba kamar irin yunkurin da Morocco ta yi a Qatar ba wanda zai kara karfafa fatan samun karin wakilci a gasar da za a yi a nan gaba.

Morocco ta fitar da Belgium, Spain da Portugal -- dukkansu a jerin kasashe 10 da ke kan gaba a wasan kwallo na duniya – inda suka zama kungiya ta farko a Afirka da ta kai zagayen hudu na karshe, kuma a ranar Laraba ne za su kara da Faransa mai rike da kofin.

Kamaru ta doke Argentina mai rike da kofin gasar cin kofin duniya da aka yi a Italiya a shekarar 1990 inda ta kai wasan daf da na kusa da na karshe. Haka kuma Senegal ma ta yi wa Faransa a lokacin da ta fara kare kambunta a shekarar 2002.

Aljeriya ta ba yammacin Jamus kashi da ci 1-0 a a shekara ta 1982. Shi ma yana daya daga cikin sakamakon da ya ba da mamaki a gasar.

'Yan wasan Morocco
'Yan wasan Morocco

Masar dai ita ce ta farko a Afirka a shekarar 1934 da ta sami shiga gasar, karkashin kocin Scotland James McCrae, amma bayan wasa daya suka koma gida, inda suka sha kashi a hannun Hungary da ci 4-2 a Naples.

Yawancin kasashen Afirka a lokacin suna karkashin mulkin mallaka ne a yayin da gasar cin kofin duniya ta zagayo bayan yakin duniya na biyu amma da kasashen suka samu 'yancin kai, hakan ya sa mambobin CAF suka karu kuma Afirka ta fara murza leda.

Nahiyar ta kaurace wa gasar cin kofin duniya da aka yi a Ingila a shekarar 1996, saboda rashin baiwa Afrika damar shiga wasan karshe na zagayen 'yan 16 -- dole aka ce sai ta buga wasa daya da kungiyoyin Asiya da Oceania – sun kuma kaurace ne don nuna adawa da shigar Afirka ta Kudu mai mulkin wariyar launin fata cikin gasar.

Kocin Morocco Walid Regragui
Kocin Morocco Walid Regragui

A shekarar 1970 ne aka baiwa Mexico damar shiga gasar inda Morocco ta kare a matakin rukunin, duk da cewa ta yi kunnen doki da Bulgaria a wasansu na karshe.

Zaire wanda ta zama Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a yanzu, an yi mata ba'a a shekara ta 1974 yayin da ta sha kashi a duka wasanni ukun da suka buga da ya hada da na Yugoslavia da ci 9-0.

Nasarar da Tunisia ta yi ta doke Mexico da ci 3-1 a Argentina a shekarar 1978 ya taimaka matuka wajen dawo da martabar Afirka kuma a shekarar 1982 kungiyoyi biyu suka yi rashin sa'a - Kamaru ta koma gida bayan da suka yi kunnen doki sau uku, sannan Algeria ta fice bayan Jamus ta Yamma ta doke Austria da ci 1-0 a wani sakamakon da aka yi zargin cewa an yi zamba ne, wanda ya sa 'yan wasan arewacin Afirka suka zo na uku a rukunin.

Jamusawan sun zira kwallo da wuri kuma wasan ya ci gaba da tabarbarewa zuwa karshen wasan. Bayan haka ne, FIFA ta yanke hukuncin buga wasanni biyu na karshe na kowane rukuni a lokaci guda don guje sake maimaita irin wannan magudi.

Morocco ita ce ta farko daga Afirka da ta samu tikitin zuwa mataki na biyu a Mexico a shekarar 1986, inda ta doke Portugal da ci 2 a rukuninsu, gaba da Ingila.

Kamaru ta sami ci gaba zuwa zagaye 'yan takwas (quarter finals) a shekarar 1990, lamarin da ya dauki hankulan duniya, musamman ma zura kwallaye daga hannun Roger Milla mai shekaru 38, wanda shugaban kasar ya ba da umarnin shigar da shi.

Wannan nasarar ta nuna alamun cewa Afirka ba za ta dauki lokaci mai tsawo ba wajen fitar da wanda ya lashe gasar cin kofin duniya, amma Senegal a 2002 da Ghana a 2010 ne kadai suka samu damar zuwa zagayen 'yan takwas.

Yayin da Afirka ta Kudu ta karbi bakunci a shekarar 2010, Afirka na da kungiyoyi shida amma Ghana ce kawai ta tsallake zuwa zagayen farko, inda aka hanata shiga zagayen kusa da na karshe sakamakon wata takaddama da dan wasan Uruguay Luis Suarez ya janyo.

Hakan ya kara tabarbarewa a kasar Rasha a shekarar 2018 lokacin da babu wasu kungiyoyin Afirka ko daya da suka kai zagayen 'yan 16.

Amma nasarar Morocco na 2022 ya canza yanayi kuma za a cigaba da murnar nasarar kasar har zuwa shekaru masu zuwa.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG