A shirye Vladimir Putin yake ya tattauna kan yiyuwar tsagaita wuta a Ukraine tsakaninsa da Donald Trump sai dai ya rushe batun sakin yankunan daya mamaye sannan ya jaddada cewa dole mahukuntan birnin Kyiv su jingine aniyarsu ta shiga rundunar tsaro ta NATO, kamar yadda wasu majiyoyi 5 dake da masaniya game da ra’ayin mahukuntan fadar Kremlin suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters.
Zababben Shugaban Amurka Trump, wanda ya sha alwashin kawo karshen yakin cikin hanzari, zai sake komawa fadar White House a dai dai lokacin da tasirin Rasha ke karuwa. Moscow na iko da wani katafaren yankin Ukraine kwatankwacin girman jihar Virginia ta Amurka kuma ta na ci gaba da fadada mamayarta cikin sauri tun bayan mamayar da ta fara a farkon shekarar 2022.
A cikakken rahoto na farko game da abin da Shugaba Putin zai amince da shi a yarjejeniyar da Trump ke kokarin kullawa, tsaffin jami’an Rasha da masu ci su 5 sun ce fadar Kremlin na iya amince ta dakatar da yakin a dai dai fagagen daga data kai a halin yanzu.
Za a iya samun damar tattaunawa a kan ainihin inda da za a yanka daga cikin yankunan gabashin Ukraine 4 da suka hada da Donetsk da Luhansk da Zaporizhzhia da kuma Kherson, a cewar mutane 3 da suka nemi a sakaya sunayensu a kan tattauna batutuwa da suka shafi tsaro.
Reuters
Dandalin Mu Tattauna