Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Rasha Na Zaman Makoki Bayan Hare-Haren Da Suka Kashe Mutane 19 A Yankin Dagestan


Russia - Harin Dagestan
Russia - Harin Dagestan

Yankin Dagestan da ke kudancin kasar Rasha ya gudanar da zaman makoki na kwanaki uku a yau Litinin bayan wani harin da mayakan Islama suka kai inda suka kashe mutane 19.

Yawancin wadanda aka kashe 'yan sanda ne, an kuma kai hari kan gidajen ibada a wasu hare-hare da aka kai a garuruwa biyu.

Rikicin na ranar Lahadi shi ne na baya-bayan nan da jami'ai suka dora laifin a kan masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama a yankin da akasarin mazauna Musulmai ne a yankin Arewacin Caucasus, kuma shine mafi muni a Rasha tun cikin watan Maris, lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude wuta a wani wurin shagali a wajen birnin Moscow, inda suka kashe mutane 145.

Wani reshen kungiyar IS ne ya dauki alhakin harin na watan Maris, sai dai babu wanda ya kai ga daukar alhakin kai hare-haren na ranar Lahadi a babban birnin yankin na Dagestan na Makhachkala da kuma kusa da Derbent, da ke kusa da tekun Caspian.

Hayaki a Dagestan
Hayaki a Dagestan

Shugaba Vladimir Putin ya nemi dora wa Ukraine laifin harin da aka kai a watan Maris, ba tare da wata shaida ba kuma duk da ikirarin da kungiyar IS ta yi. Kyiv ta musanta hakan cikin kakkausar murya.

Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya ce Putin ya samu rahotanni game da hare-haren na ranar Lahadi da kuma kokarin taimakawa wadanda abin ya shafa.

Russia
Russia

Kwamitin binciken, babbar hukumar binciken manyan laifuka ta kasar, ta ce an kashe dukkan maharan biyar. Daga cikin mutane 19 da aka kashe, 15 ‘yan sanda ne.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG