Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Yace Rasha Zata Mai Da Kwakwaran Martani Idan Amurka Da Kawayenta Na NATO Suka Sahalewa Ukraine Amfani Da MaZile A Rasha


FILE PHOTO: Russian President Putin chairs a meeting on the social and economic development of Crimea and Sevastopol, in Moscow
FILE PHOTO: Russian President Putin chairs a meeting on the social and economic development of Crimea and Sevastopol, in Moscow

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce zata mai da kakkausar martani biyo bayan hasashen cewa Ukraine zata kai mata farmaki da makamai masu cin dogon zango.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce Moscow zata dau “wasu jerin matakan martini” har idan Amurka da kawayenta na NATO suka amince Ukraine ta kai hari cikin Rasha da makamai masu cin dogon zango, bisa kalaman aka wallafa da aka ce ya furta a ranar Lahadi.

Ma’aikatar tsaron Rasha tana duba irin martanin da zata mai game da hasashen kai mata farmaki da makamai masu cin dogon zango, "zata mai da martini mabanbanta” amsar da Putin ya baiwa wani dan jarida Pavel Zarubin kenan, cikin wani faifaiyin bidiyon da aka kafa a adireshin Zarubin na manhajar aike sakonni ta Telegaram.

Sannan, na’urorin kare hare haren saman Rasha sun kakkabo jiragen Ukraine marasa matuka 51 cikin dare, a cewar ma’aikatar tsaron Rasha da sanyin safiyar Lahadi.

An kakkao jirage marasa matuka 18 a yankin Tambov, wanda ke da ratar kilomita 450 zuwa kudu maso gabashin Moscow, abinda ma’aikatar tsaron ta wallafa ta Telegram Kenan. An kuma kakkabo wasu jirage marasa matukan guda 16 a yankin kan iyakar Belgorod sannan sauran kuma a yankunan Voronezh, Oryol, da Khurks a kudancin Rasha.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Tsofaffi Ke Fama Da Lalular Yanar Ido A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG