Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Portugal Ta Doke Ghana Black Stars Da Ci 3-2 

Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2
Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2

Tawagar kwallon kafa ta Portugal ta yi nasarar doke Ghana da ci 3-2 a karawar farko da suka yi a rukunin H a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022 da ke gudana a kasar Qatar.

KUMASI, GHANA - Tauraron ‘dan wasa kyaftin din Portugal Christiano Ronaldo ya zura kwallon farko a ragar tawagar Ghana Black Stars ta bugun fenarati a minti na sittin da biyar kafin Andre Dede Ayew ya farke ta a minti na saba'in da uku.

Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2
Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2

Sai dai wasu mintuna kadan bayan farkewar da Ghana ta yi, Portugal ta kara zura kwallaye biyu a ragar tawagar Ghana Black Stars abin da ya kai adadin kwallayenta uku a wasan, kafin dan wasan gaban tawagar Ghana Black Stars Usman Bukari ya zura kwallo na biyu a minti na tamanin da tara.

Jama'a da dama ciki harda wasu ‘yan kasashen waje masu zama Ghana ba su ji dadin matakin da alkalin wasan kwallon ya dauka na bai wa Portugal bugun fenarati ba.

Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2
Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2

Wani dan Najeriya mai suna Dan Liti mai zama Ghana ya fada wa Muryar Amurka cewa. " gaskiya wasan da a ka yi a yau tsakani da Allah Ghana sun yi kokari, kuma sun yi abin da ba a zata ba. Sai dai abin da ya faru shine alkalin wasan yadda ya yanke hukunci na bai wa Portugal fenarati na daga cikin abubuwan da ya kawo cikas a wasan".

Wasu 'yan Ghana sun zargi mai horar da tawagar Ghana Black Stars Otto Addo da tafka kuskure wajen sauya wasu 'yan wasa kamar Kudus Muhammad tare da kyaftin din tawagar Andre Dede Ayew a inda suke cewa matakin yayi sanadin karin kwallaye biyu da aka zura a ragar Black Stars.

Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2
Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2

Shi kuwa Muhammad Awal mai sharhi kan harkar kwallon kafa a Ghana na ganin matakin da kocin ya dauka shi ne mafi a'ala sabida Kudus Muhammad, duk da kokarinsa, ya na da katin gargadi adon haka muddan ba a sauya shi ba komai na iya faruwa. Mallam Awal ya jinjina wa Ghana bisa kokarin da ta yi a inda yake cewa alkalan wasan ciki da na dakin VAR ne ba su taimaka ma Ghana ba.

Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2
Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2

Ghana ce tawagar Afirka ta farko da ta zura ƙwallo a raga zuwa yanzu a wannan gasar, bayan Kamaru da Senegal da Maroko da Tunisiya sun gaza yin hakan.

Ghana za ta kara da Koriya ta Kudu a wasa na gaba ranar 28 ga watan Nuwamba, inda Portugal za ta kara da Uruguay.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Portugal Ta Doke Tawagar Ghana Black Stars Da Ci 3-2 .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG