A minti na 82 da fara wasa Gareth Bale ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, lamarin da ya mayar da hannun agogo baya ga kwallon da Tim Weah ya ci wa Amurka a farko a karawar da ta yi da Wales.
Hakan ya sa kasashen biyu suka tashi da ci 1-1 a gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar.
Weah, wanda dan tsohon gwarzon kwallon kafa na FIFA kuma shugaban kasar Laberiya na yanzu George Weah ne, ya zura kwallo a raga bayan da Christian Pulisic ya doko masa kwallon a minti na 36 da fara wasa.
Amurka dai ba ta samu zarafin zuwa gasar ta cin kofin duniya a 2018 ba, amma ga dukkan alamu a wannan karon, tawagar ‘yan wasan kasar sun zo da shirin samun nasara.
Wales dai ta samun bugun fenariti ne, bayan da Walker Zimmerman ya kwade Bale ta baya, kuma alkalin wasa Abdulrahman Al-Jassim na kasar Qatar mai masaukin baki, bai yi wata-wata ba ya nuna bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Bale ya zura kwallonsa a hannun hagu na hannun mai tsaron gida Matt Turner, inda ya ci kwallo ta 41 a wasanni 109 da ya buga a duniya, inda ya samawa Wales maki a wasan farko na gasar cin kofin duniya da ta buga tun bayan shekara ta 1958.