Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), a zaben 2023, Peter Obi, ya yi Allah wadai da kalaman kyamar kabilar Yarbawa da wata ‘yar kabilar Igbo da ke zaune a Canada, Amaka Patience Sunnberger ta yi.
Sunnberger a cikin wani faifan bidiyo da ya kaarde shafukan sada zumunta ta yi barazanar yin amfani da sinadirai (guba) masu cutarwa akan ’yan Najeriya ‘yan kabilar Yarbawa ko Bini.
Biyo bayan furacin na ta ne, shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa ta bayyana sunan matar, sannan ta bukaci gwamnatin Canada da ta gurfanar da ita a gaban kuliya.
Da yake mayar da martani game da batun a cikin wasu jerin kalamai a kan shafin X a ranar Juma'a, Obi ya bayyana furacin Sunnberger a matsayin jiji da kai da ya wuce gona da iri.
Obi ya ce bai kamata irin wadannan maganganu na raba kan jama’a su samu gurbi a cikin al’ummarmu ba, shi ya sa kuma kowa ya yi watsi da shi.
“Na yi Allah wadai da kalaman nuna kyama da ayyukan da aka danganta ga wata mace ‘yar kabilar Igbo da ke zaune a kasar Canada akan ‘yan kabilar Yarbawa ko Benin. Irin wadannan maganganu ko halayya masu raba kan jama’a ba su da wani matsayi a cikin al’ummarmu.’
"A matsayinmu na 'yan Najeriya, ya kamata mu hada kai mu mai da hankali kan magance kalubalen da muke fuskanta, maimakon barin kabilanci da kiyayya su raba mu."
Dandalin Mu Tattauna