Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Bayyana Matsayarmu Kan Hukuncin Kotun Zabe - Jam'iyyar LP


Magoya bayan jma'iyyar LP a Najeriya
Magoya bayan jma'iyyar LP a Najeriya

Jam'iyyar ta LP ta ce za ta tuntubi lauyoyinta kan mataki na gaba da za ta dauka kan hukuncin.

Jam’iyyar adawa ta Labour Party a Najeriya, ta yi fatali da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke kan korafe-korafen da ta shigar kan nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar jim kadan bayan sanar da hukuncin, sakataren yada labarai Obiora Ifoh ya ce ba za su amince da daukacin hukuncin ba.

“’Yan Najeriya suna kallo yadda aka yi mana fashin zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, zaben da duniya ta yi Allah wadai da shi, amma kotun zaben a irin tata mahangar ta ki amincewa da gaskiya.” Ifoh ya ce.

Kotun zaben ta yi watsi da korafin da jam’iyyar LP da dan takararta Peter Obi suka shigar inda suke kalubalantar INEC dangane da yadda ta ki fitar da sakamakon zaben ta yanar gizo.

Kotun har ila yau ta yi watsi da ikirarin da jam’iyyar ta LP da Obi suka yi na cewa ana bukatar dan takarar ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a Abuja, babban birnin kasar.

“Jam’iyyarmu za ta fitar da matsaya bayan mun tuntubi lauyoyinmu idan muka karbi asalin kwafin hukuncin. Sanarwar Ifoy ta ce wacce aka wallafa a shafin jam’iyyar na Facebook.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG