WASHINGTON DC - Dan takarar shugaban kasar jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, yayi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai dasu rage almabazzaranci tare da yin amfani da kudade wajen fitar da al’umma daga kangin talauci.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma bukaci ‘yan Najeriya masu hannu da shuni su hada hannu da shi wajen samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, cikin abubuwan more rayuwar da ‘yan Najeriya ke matukar bukata.
A cewarsa, kiran samar da ruwan shan ya zama wajibi kasancewar kamfar ruwan ce ta sa shi haka rijiyoyin burtsatse guda 10 a arewacin Najeriya tare da niyyar sake haka karin wasu 10.
Haka kuma Peter Obi ya bada gudunmowar Naira milyan 10 ga wata makarantar almajirai kuma yana da niyar bada irin wannan gudunmowa ga wasu makarantun 2.
Tsohon gwamnan ya kara da cewar yana da mahimmanci mu magance kalubalen da muke dasu a yau amma abu mafi mahimmanci yin kyakkyawan shiri domin tunkarar gobe.
Ya kuma bada shawarar cewar karatun allo na iya tafiya kafada da kafada da na zamani a aji guda.
Sakamakon hirarsa da manema labarai wacce ya wallafa a shafinsa na x, Peter Obi ya jaddada bukatar zuba jari a bangaren kiwon lafiya ta hanyar bada horo da kwarin gwiwa ga ma’aikatan jinya.
Dandalin Mu Tattauna