Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP ta Zama Jam'iyyar Adawa a Majalisar Wakilan Najeriya


Wasu gwamnonin da suka fara yiwa jam'iyyar PDP tawaye
Wasu gwamnonin da suka fara yiwa jam'iyyar PDP tawaye

Sabili da canza sheka da wakilai da suka fito daga jihohin da gwamnoninsu suka fice daga PDP yanzu jam'iyyar ta rasa rinjaye a majalisar wakilai.

'Yan majalisa da suka canza sheka daga PDP zuwa jam'iyyar adawa ta APC sun fito ne daga jihohin da tuni gwamnoninsu suka fice daga maj'iyyar PDP, wato jihohi biyar da suka hada da Rivers da Kano da Kwara da Sokoto da Adamawa.

Wannan canza shekar ta baiwa jam'iyyar APC rinjaye a majalisar wakilai inda a yanzu tana da wakilai 172 yayin da PDP ke da wakilai 171. Mustapha Dawaki dan majalisar wakilai ne da aka zaba daga jihar Kano karkashin jam'iyyar PDP ya bayyana hujjarsa ta canza sheka. Ya ce rashin kula da gaskiya da kula da 'yan jam'iyya da PDP ke yi da rashin nuna amana da jiji da kai su ne suka sa ya yi watsi da PDP. Harkar jam'iyya kuma mutum nada 'yanci ya bar wata jam'iyya zuwa wadda ya ga ta dace. Sabili da haka suka ga ya dace su bar PDP su shiga APC sabo da suna ganin APC zata yi masu adalci. APC zata kula da mutanen Najeriya. Ya ce amma abun da PDP keyi zata wargaza Najeriya gaba daya.

Shi ma Ado Doguwa dan PDP ne a da ya kuma bada dalilan da suka sa ya bar jam'iyyar. Ya ce daga yau shi da jama'arsa a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano duk sun koma APC sabili da milkin kama karya da jam'iyyar ke yi.

Wani da ya dade a jam'iyyar APC daga jihar Gombe Hanis Mailantarki ya ce yana murna da karbar sabbin shiga jam'iyyar APC. Ya ce duk wani mai son gaskiya a kasar Najeriya ba zai goyi bayan wannan gwamnatin ba. Tun da ta fara kawo yanzu an ga irin halin da kasar ta shiga. Kasar tana bukatar gyara kuma jam'iyyar APC ta tanadi shirin yin gyara da zai kyautatawa jama'ar kasar.

Cikin 'yan wakilai 37 da suka koma APC 18 sun fito ne daga jihar Kano. To idan an hadasu da 13 da tun ainihi suna cikin APC wato duk 'yan majalisu daga jihar Kano sun zama 'yan APC. Haka ma 10 daga cikin 11 daga jihar Sokoto ban da kakakin majalisar duk sun koma APC. Takwas daga cikin 13 da suka fito daga jihar Rivers 'yan APC ne yanzu. Kana 6 daga jihar Kwara sun koma APC. Biyar daga cikin 12 daga jihar Bauchi suna cikin APC yanzu. A jihar Katsina kuma 13 daga cikin 15 sun koma APC.

Medina Dauda nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG