Wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin jam'iyyu da kantamonin riko da shugabannin al'umma da jami'an tsaro domin fadakar dasu dangane da shirin hukumar na kara kirkiro mazabu a duk fadin jihar.
To sai dai shugabannin siyasa sun fi damuwa ne da lokacin da za'a yi zaben kananan hukumomi mai inganci da kuma adalci. Abdullahi Shehu shugaban APC a jihar Bauchi ya ce basu da karfin gwuiwa a zaben kananan hukumomi domin kwamitocin riko da gwamnati ta kafawa duk kananan hukumoni da aka sani da sunan kiyateka. Mutanen da aka sa kiyateka mutane ne da ko zaben kofar gidansu ba zasu iya ci ba to amma tun da suna kan kujerun iko suna iya karkata akwatunan zabe su yi abun da suke so.
Sani Malam na jam'iyyar APC ya ce idan dai zabe ne za'a yi ya yi imani ba za'a yi adalci ba a duk fadin jihohin Najeriya. Ya ce ya gani kowane gwamna dake kan mulki jam'iyyar hamayya ko kansilo daya ba'a bari ta ci. Ya ce gara ma mutane su huta da ransu. Su huta da batun zaben kananan hukumomi domin bashi da wani anfani kuma bashi da wani riba ga talakan Najeriya.
Kwamishanan zabe na jihar Bauchi Abdulmunmuni Mohammed ya bayar da tabbacin zasu gudanar da zabe mai inganci da adalci kana ya roki shugabannin jam'iyyu da su zaburar da magoya bayaansu su fito su yi zabe lokacin zaben. Ya ce komi ana yi ne daki daki. Yanzu an ce za'a kara mazabu don haka sai a taimakesu da addu'a. Idan sun samu kayan aiki isassu zasu shirya zaben kananan hukumomi ba tare da kara wasu kwanaki ba. Ya ce ba sun zo ba ne su yaudari jama'a.
Ga rahoto.