Wannan sanarwa ta biyo bayan ganawar da sassan biyu suka yi a masaukin gwamnatin Jihar Kano dake Abuja.
Koda yake sanarwar ba ta yi nuni da cewa gwamnonin na PDP-Sabuwa sun koma cikin jam'iyyar APC kacokam ba, da alamun wannan matakin, raba hanya ce baki daya da jam'iyyar PDP-Tsohuwa dake karkashin jagorancin Bamanga Tukur da shugaba Goodluck Jonathan.
Sanata Hadi Sirika, yace matakan nuna kama-karya da cin zarafin da ake yi ma gwamnoni 7 na PDP da suka nuna rashin jin dadinsu da wasu abubuwan da suke faruwa cikin jam'iyyar tasu, da kuma mayarda su 'yan adawa na karfi da yaji, su suka janyo hakan.
Sanata Sirika yace karfin masu hamayya a Najeriya a wannan lokacin, ya shige gaban barazana. Ya ce, tura ta kai mutane bango ne, shi yasa ake ganin irin wannan wutar sauyi na kunnuwa a Najeriya.
Mai ba shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, yace ai ba wai shugaban ba ya son zama ya tattauna da gwamnonin 7 ba ne, tafiyar da yayi ta sa bai samu zama ya tattauna da su ba. Haka kuma ya musanta cewa gwamnati tana amfani da hukumomi irinsu EFCC wajen cin zarafin masu korafin.
Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko mana da karin bayani.