Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan: Jami'ai Sun Hallaka 'Yan Kungiyar Taliban da Dama


Frayim Ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani
Frayim Ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani

A cigaba da fafatawa da kungiyar Taliban Pakistan ta sanarda hallaka yan kungiyar da dama yau Juma'a akan iyakarta da Afghanistan mahaifar kungiyar ta Taliban.

Jami’an soji a Pakistan sunce an kashe akalla ‘yan bindiga 20 a yau Juma’a, a wani hari da aka kai musu ta sama a inda suke boye can Arewa maso yammacin iyakar kasar.

A cikin wata ‘yar gajeruwarsanarwa da suka bayar suka ce jiragen yakin kasar sun auna wasu wurare masu nisa a yankin Khyber mai kabilu da ke kusa da iyakar Afganistan. Sanawar ta ‘kara da cewa kimanin ‘yan bindigar 18 ne suka raunata.

Garin na Khyber dai ya zamanto hanya daya daga cikin hanyoyin biyun da ake iya amfani da su wajen shige da fice tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Ba’a dade ba sojojin Pakistan suka kori ‘yan kungiyar Taliban na Pakistan daga yankunan su. Jami’ai sun tabbatar da korar ‘yan bindigar da ga yankunan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG