Kakakin ma’aikatar tsaron Najeriya Birgediya Janal Rabe Abubakar, shine ya tabbatar da cewa har yanzu ana kai hare haren a wasu yankunan jihahin Ogun da Lagos, a tattaunawarsa da wakilin Muryar Amurka Hassan Umar Tambuwal. Haka kuma ya tabbatar da cewa har yanzu sojoji suna gudanar da aikin tsaro da ake yiwa take da suna Operation A Watse, wanda kuma ke ci gaba da samun nasara.
Yanzu haka dai sojoji na samun nasara a kan ‘yan kungiyar Niger Delta dake yankunan a jihohin Lagos da Ogun, Janal Rabe ya musunta rahotannin dake cewa har yanzu wasu tsagerun dake wadannan yankuna na cin karensu ba babbaka, ya kuma tabbatar da cewa tun lokacin da aka gudanar da Operation A Watse, aka taka musu birki sai dai wasu abubuwa da ba a rasa ba.
Sojojin Najeriya zasu kasance a wannan yanki domin tabbatar da cewa babu wani sauran tashin hankali. Daga karshe Janal Rabe, yayi kira ga al’umomin yankin da su hada kai da jami’an tsaro don tabbatar da cewa bata gari da ‘yan ta’adda basu dawo yankunan ba.
Domin karin bayani.