Babban sakataren gidauniyar Dr Abdullahi Baffa shi ya bayyanawa manema labarai hakan yayinda ya kai ziyarar gani da ido a harabar jami'ar.
Dr Baffa ya bayyana takaicinsa kan irin barnar da wutar tayi a babban dakin karatun na jami'ar. Yace gobarar ta yi masu barna ba kadan ba. Duk littafan dake ciki da naurorin kwamfutoci dukansu suka kone. Ba'a ma batun kujeru da sauran kayayyakin dake ciki
Dr Baffa yace ba karamin tashin hankali ba ne a wurinsu, musamman ga hukumarsu wadda ta kasance itace take samarda tallafi domin bunkasa ilimi mai zurfi a kasar.
Dangane da tallafin da hukumar zata bayar, Dr Baffa yace mafi karancin abun da zasu yi shi ne "duk abun da ya kone mu dawo masu dashi", inji Dr Baffa. Duk abun da ya lalace zasu gyara. Zasu yi duk abun da zasu yi dakin karatun ya koma kamar ba'a yi gobara ba.
Shi ko shugaban jami'ar Farfasa Sebastine Maimako yace duk da yake ba zai iya bada adadin hasarar da aka yi a gobarar ba, amma sun bukaci manyan malaman jami'ar kowannensu ya bada miliyan guda guda yayinda sauran malamai da dalibai zasu bada tasu gudummawar.
Shugaban yace littafan ba suka kone sun kai dubu tamanin banda wadanda suke sassa daban daban.
Wasu daliban da aka zanta dasu sun bayyana irin matsalar da suka shiga wajen yin karatu sanadiyar gobarar.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.