Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Zata Warware Matsalar Batun Ciwo Bashi


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Bayan majalisar dattawan Najeriya tayi fatali da bukatar shugaba Buhari na ciwo bashin dalar Amurka biliyan talatin saboda cewa gwamnati bata bi ka'idoji ba yanzu gwamnatin ta dukufa domin warware matsalar tare da bin ka'idojin da suka dace.

Abun kunya ne a ce gwamnati bata san matakan da ya kamata ta dauka ba idan zata gabatar da irin wannan bukatar wa majalisun kasar.

Yanzu ya zama wajibi tayi abun da ya dace kuma hakan tace zata yi. Zata dauki sabbin matakan gamsar da 'yan majalisa domin su samu cikakkun bayanan da suke nema kafin su yanke shawara akan ciwo lamunin.

Ministar tsare-tsare da kasafin kudi Hajiya Zainab Samshuna tayi karin haske dangane da abun da ya faru. Tace bata san abun da ma'aikatar kudi tayi ba domin itace ta kai bukatar. Tace yanzu ya kamata a zauna da jami'an ma'aikatar a tantance abubuwan da suka kamata a yi kana a sake maida masu a majalisa.

Hajiya Zainab tace bashin ba na gwamnatin tarayya kadai ba ne. Akwai basussuka na jihohi daban daban da suka shirya da bankin duniya da bankin musulunci. Karin bayanan da za'a nema a hada zai fito ne ma daga jihohin.

Shi kuwa ministan sufuri na Najeriya yace duk kace nace din ba wani babban matsala ba ce domin za'a tabbatar an gamsar da 'yan majalisa ta fuskar tattaunawa dasu da kuma bin duk ka'idojin da aka gindiya. Yace gwamnati zata basu abubuwanda suka tambaya.

Ministan yace suna son 'yan majalisa su fahimta cewa bashin domin kasar ne ba wai wani ne zai cinye kudin ba. Dole ce ta sa za'a karbo bashin.

Malam Sha'aibu Idris kwararre akan harkokin tattalin arziki cewa yayi abun da ya faru abun kunya ne domin ya nuna wasu manyan jami'an gwamnatin Buhari basu san aikinsu ba, yana mai cewa wajibi ne a yi masu hukunci. Ya kira shugaban kasa ya ladaptar da mukarabansa da suke shafa masa kashin kaza.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG