An gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, wanda ya mayar da hankali ne akan ayyuka da gudunmawar jagororin kafa daular Usmaniyya, kamar Shiek Usmanu Bin Fodiyo da kaninsa Abdullahi Gwandu da kuma ‘ya ‘yansa Mohammadu Bello da Nana Asma’u, musamman dangane da abin da ya shafi ilimi da siyasa da shugabanci dama harkokin tattalin arziki da kiwon lafiya.
Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar, cewa yayi rashin adalci a shugabanci na daya daga cikin matsalolin da ke kawo tarnaki ga ci gaban Najeriya, mai alfarma sarkin musulmi ya bayyana damuwa kan yadda zababbun shugabanni na siyasa musamman gwamnonin jihohi ke kashe makurden kudade wajen aiwatar da ayyukan da basu da alfanu ga rayuwar talaka.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, wanda ya kaddamar da bude taron ya mayar da hankali ne ga irin namijin kokarin da mai alfarma sarkin musulmi yake yi a cikin shekaru 10 da ya yi yana mulki, wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da fahimtar juna tsakanin yan Najeriya, musumman tsakanin mabiya addinai biyu na Musulunci da Kristanci. Haka kuma yayi sharshi sosai akan gudunmawar da jagororin daular Usmaniya suka bayar wanda yace har yanzu suna amfanar da Najeriya a zamanta na kasa daya.
Masana daban daban ne daga Najeriya da ketare har ma da kasashen turai ne suka gudanar da makala a lokacin taron.
Domin karin bayani.