Muryar Amurka ta fara zantawa da mazauna sansanin wadanda kuma suka nuna godiyarsu saboda suna samun ci da sha ba tare da matsala ba.
'Yan gudun hijiran sun nuna farin cikinsu da ziyarar tawagar majalisar dattawan Najeriya da ta zo ta gani ma idonta yadda suke.
Kafin ziyarar, hukumomin Najeriya sun fara binciken zargin cin zarafin mata a wasu sansanin 'yan gudun hijira kamar yadda Human Rights Watch ta ruwaita a wani rahoto da ta fitar wa duniya. Tayi zargin ana lalata da matan da rikicin Boko Haram ya daidaita da suke sansanonin.
A cewar Human Rights Watch an ci zarafin matan ne ta yi masu fyade tare da yaudararsu. Jami'an gwamnati da suka hada da hukumar NEMA sun ce zasu cigaba da binciken lamarin.
Sanata Abdulaziz Nyako shugaban tawagar yace sun damu da 'yan gudun hijiran ba wai sun manta dasu ba ne domin sun je Abuja.Yayi masu alkawarin sake dawowa su gansu. Yace su ma 'yan Najeriya ne kuma duk abun da ya shafi 'yan Najeriya ya shafesu dole ne kuma su kawo taimako.
Yanzu dai a jihar Adamawa 'yan gudun hijira dubu goma sha takwas ne suka saura daga dubu sittin.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.