Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya soki shugabannin kasashen turai da zama kanwa uwar gamin da suka janyo matsalar bakin haure da suke korarowa zuwa turai.
Mr. Obasanjo, ya furta hakan ne a cikin wata budaddiyar wasikar da ya aikewa shugabannin kasashen turai. Yace rashin tsayayyiyar shugabanci a Libya itace ta janyo wannan matsala.
Tsohon shugaban na Najeriya yace ya tuna a shekara ta 2002, sun zauna da shi da tsoshon shugaban na Libya Kanal Moammar Gadhafi, suka yarda cewa Libya zata hana matasa da suke bi ta cikin kasar tafiya turai, kuma daga bisani ya maida su kasashensu na asali.
Amma tunda shugabannin turan suka hada baki suka kashe Moammar Gadhafi, shekaru hudu da suka wuce, kasar take cikin matsalolin shugabanci, saima kara tabarbarewa al'amarin yake yi maimakon ya gyraru.
Da yake sharhi kan wasikar ta tsohon shugaba Obasanjo, wani masanin harkokin kasa da kasa Dr. Alharun Mohammed, yace Mr. Obasanjo yayi gaskiya, domin ba don halaka Gadhafi ba, da wuya ace Libya ta zama hanyar da bakin hauren suke bi domin zuwa turai, baya ga haka, matsalar ta Libya tana ci gaba da barazana ga sauran kasashen Afirka.
Daga nan Dr.Mohammed, yayi kira ga kungiyar hada kan kasashen Afirka watau (AU) takaice, ta kira wani taro na musamman domin daukar mataki kan wannan rikici a Libya, da kuma korarda bakin haure suke yi.