Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce zai iya sadaukar da rayuwarsa ga kasar amma banda wata jam’iyyar siyasa saboda Nijeriya ta fi duk wani mutum muhimmanci. Obasanjo ya yi wannan maganar ce ya yin da tawagar dan takarar Shugabancin Nijeriya karkashin jam’iyyar NCP ta kai ma sa ziyara.
Kan haka ne abokin aikinmu Ladan Ibrahim Ayawa yay a yi hira da wani mai fashin baki mai suna Dr. Abbati Bako, wanda ya ce kalaman na Obasanjo sun ta’allaka kan abubuwa biyu. Ya ce da farko dai ga dukkan alamu, Obasanjo na jin kunya da kuma shakkun yiwuwar cimma gaci na ciyar da Nijeriya gaba saboda tsohon Shugaban kasa ne, wanda ya san jam’iyyarsu sosai ya kuma ya san kasar sosai.
Na biyu kuma, ya ce da alamar ana so a samu daidaito a sha’anin dimokaradiyya a Nijeriya. Ya ce kuma akwai wasu ‘yan kasashen waje da ke da ruwa da tsaki a Nijeriya saboda kadarorinsu da sauran muradunsu, wadanda a kullum su kan ankarar da Nijeriya da zarar sun ga alamar wata babbar matsalar siyasa ko zamantakewa.