Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, sun gana na tsawon lokaci domin tattauna matsalolin tsaro da suka dabaibaye Najeriya a daidai wannan lokacin.
Da yake tabbatar da wannan ganawa ta su ga masu neman labarai, Janar Babangida ya ce ya kamata kowane dan Najeriya ya sanya hannu a kokarin kawo karshen wannan ukuba da ta far ma kasar.
A wata hirar da yayi da wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, janar Babangida ya ce zasu ci gaba da wannan kokari nasu, kuma ko da ta kama ne ma, zasu sake sanya rigunansu na soja domin tabbatar da ci gaba da dorewar Najeriya a zaman kasa daya.
Ga bayanin Janar Babangida a wannan hira ta su...
Batun Tsaro A Najeriya Hira Da Janar Ibrahim Badamasi Babangida |