Tattaunawar da Shugaba Obama ya yi da Shugaba Jonathan ranar Litinin ta maida hankali ne kan kalubale da ta’adanci ke yi ma kasashen Afirka har da Najeriya inda kasar na fama da yakar kungiyar Boko Haram.
Shugaban ya ce Amurka zata cigaba da taimakon Najeriya ta karfafa iyawarta yadda zata kalubali matsalolinta wadanda Shugaba Obama ya kira munanan kalubale ga harakar tsaro.
Amma harin da aka kai kan katafaren gini shaguna a kasar Kenya shi ne ya fi daukar hankalin jaridu da wasu kafofin labaru.
Shugaba Obama ya ambato tadin da ya yi da Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta wanda ya rasa ‘yanuwa a harin. Ya ce Amurka tana tare da al’ummar Afirka kuma ta sha alwashin yin aiki da duk Afirka har sai an ga bayan ‘yan ta’ada a nahiyar.
Shugaba Obama ya ce “wannan ya sake jaddada bukatar da ke akwai cewa duk mutanen duniya su tashi tsaye tare su kawo karshen irin wannan kisan gilla na ba gaira ba dalili da mugayen kungiyoyi ke aiwatarwa” Ya ce “Amurka zata cigaba da yin aiki da nahiyar Afirka da duk duniya ta tabbatar an wargaza ‘yan ta’ada da ta’addanci”.
Da yake mayarda martani Shugaba Jonathan ya ce Najeriya da Amurka dama kawaye ne. Ya kuma ambato kokarin da kasar Najeriya ta yi na kawo zaman lafiya a yammacin Afirka da ma sauran nahiyar. Daga bisani ya ce aika-aikar da aka yi a Nairobi ya sake nunawa cewa akwai bukatar a hada karfi da karfe a yaki ta’adanci. Sabili da haka Najeriya tana bukatar karin taimako daga Amurka domin ta yaki ta’adanci.
Shugabannin sun tabo batun zaben Najeriya na shekarar 2015 inda Obama ya ce wajibi ne a tabbatar cewa zaben ya inganta manufofin Dimokradiya a kasar.
Daga karshe Obama da Jonathan sun ce yakamata a samarda wutar lantarki a duk fadin nahiyar Afirka a kuma samar ma matasa ayyukan yi domin su samu karfafawa da cin gashin kansu.
Obama zai yi jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya yau Talata.