Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Ci Gaba Da Nakkasa Kungiyar Boko Haram In Ji Jonathan


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya lokacin rufe taron kolin ECOWAS a Abuja, 18 Yuli, 2013.
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya lokacin rufe taron kolin ECOWAS a Abuja, 18 Yuli, 2013.

Sai dai kuma shugaban yace gwamnati ba zata yi sako-sako ba duk da cewa an samu raguwar hare-haren ta'addanci a cikin kasar.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya bayyana cewa sannu a kan hankali, matakan tsaron da gwamnati take dauka su na nakkasa karfin kungiyar nan ta Boko Haram.

Shugaba Jonathan ya bayyana wannan ne a lokacin da yake ganawa da Mr. David Mac Rae, wakili mai barin gado na Kungiyar Tarayyar Turai a Najeriya da kuma Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAs ko CDEAO.

Shugaban yace irin matakan da gwamnatinsa ta dauka sun kawo raguwar hare-haren ta'addanci sosai a cikin Najeriya. Yace gwamnati zata ci gaba da daukar matakan da zata iya domin tabbatar da tsaro a duk fadin kasar, yana mai cewa “muna sauya tsarin yadda muke gudanar da ayyukan tsaronmu a kai a kai domin takalar ta'addanci, wanda ya zamo kalubale a fadin duniya.”

Sai dai kuma shugaba Goodluck Jonathan yace duk da wadannan alamomin nasara da aka fara gani, ba zasu yi sako-sako ba, kuma ba zasu daina daukar karin matakan tabbatar da tsaro da kare lafiyar duk wani dan kasa da wadanda ke zaune a cikin Najeriyar ba.
XS
SM
MD
LG