Abokin aiki Bello Galadanchi ya zanta da masanai kan harkokin siyasa Dr. Isiyaku Aliyu domin samun amsar tambayar. A firarsu ya ce Najeriya na bin tafarkin dimokradiya ne kuma akwai tsari da aka shirya. To muddin ana bin dimokradiya ko mutum na shugabanci ko baya yi yana da 'yancin ya tsaya takara. Shugaban kasa na yanzu yana da 'yancin ya tsaya takara. Duk da wai bai fito ya ce zai tsaya ba amma idan lokaci ya yi yana da tashi jam'iyyar akwai wasu 'yan takara kuma da nasu jam'iyyun duk sai su fito su takara muddin tsarin mulki ya tanadi yin hakan.
Batun cewa domin Shugaba Jonathan ya karasa wa'adin marigayi Shugaba Musa 'Yar'Adu'a zai kawo rudani, Dr. Isyaku ya ce ba zai kawo rudani ba idan yana cikin tsarin mulkin kasar cewa yana iya tsayawa. Idan hukumar zabe ta fitar da dokokin yadda za'a yi takara zasu nuna wanda zai iya tsayawa da wanda ba zai iya ba. Sai a jira wannan lokacin.
Game da 'yan adawa dake cewa bai kamata Jonathan ya sake tsayawa ba sai Dr Isiyaku ya ce a Afirka idan kana rike da madafin iko to kana da fifiko kana 'yan hamaya. Ya ce kila tunanen 'yan adawa ke nan cewa kasancewarsa a kan karagar milki zai bashi wani matsayi da yafi nasu lamarin da ka kaishi ga sake samun nasara a zabe mai zuwa. Hadewar jam'iyyu zuwa babbar jam'iyya wata hanya ce a dimokradiya ta samun galaba kan wata jam'iyyar adawa.
Ga karin bayani.