Umarnin kungiyar ga daukacin mambobinta ya zo ne sakamakon cire tallafin man fetir da sabuwar gwamnatin kasar ta yi tun bayan shan rantsuwar sabon shugaban Kasar ta Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar ta NLC ba ta yi na’am da sabon tsarin cire tallafin ba, inda ta ayyana shi a matsayin wata bita da kulli kuma ta bukaci a yi gaggawar mayar da farashin zuwa yanda yake da.
Shugaban NLC Kwamred Joe Ajaero, da ya ke zantawa da manema labarai a taron kungiyar kwadagon ta kasa a ranar Juma’a, ya ce kungiyar ta bada umarnin yajin aiki a duk fadin kasar.
NLC ta yanke shawara har idan kamfanin NNPC bai janye sabon farashin da ya sanar a baya bayan nan ba, daga nan zuwa ranar Laraba mai zuwa kungiyar kwadagon da dukkanin magoya bayanta za su tafi yajin aikin gama gari a duk fadin kasar domin nuna rashin amincewar su da cire tallafin da aka yi, wanda su ka ce baya bisa ka’ida.