A wani yunkurin na ganin an kaucewa yajin aikin gama-gari da kungiyar kwadago ta NLC ta yi gargadin farawa a ranar Laraba, Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya gana da shugabannin kungiyar ta NLC.
A makon da ya gabata, shugaban NLC Joe Ajaero, ya ba gwamnati mako guda ta kawar da matsalar karancin kudi da ake fuskanta ko kuma ‘ya’yan kungiyar su shiga yajin aiki a duk fadin kasar.
Ministan kwadago Chris Ngige wanda ya shiga tsakani, ya gayyaci bangarorin biyu a ranar Litinin don a samu maslaha.
A karshen makon da ya gabata babban bankin na Najeriya ya ce ya saki kudade ga bankunan kasar, har ma ya umurce su da su yi aiki a karshen mako don a wadata jama’a.
Gidan talbijin na Channels TV, ya ruwaito Ajaero yana cewa yanzu babu wata matsala, tun da CBN ya ba da wannan umurani.
Bayanai daga sassan Najeriya na cewa wasu mutane sun fara samun kudadensu amma ba yadda ya kamata ba.
Hakan ya sa Ajaero ya yi kira ga hukumomin bankin na CBN da su kara kaimi wajen tabbatar da jama’a na iya kai wa ga kudadensu a duk lokacin da suke bukata.