Shugaban kungiyar Kwadago ta NCL, Komred Joe Ajero ne ya sanar da umurnin a taron kungiyar a Abuja.
Sakamakon taron ya nuna kungiyar ta gaji da bukatar da ta mikawa babban bankin Najeriya CBN, da ya wadatar da kudin amma sai kara ta'azzara lamarin ya ke yi.
Sakataren tsare-tsare na kungiyar Komred Nasir Kabir ya ce 'yan kungiyar za su mamaye ofisoshin babban bankin, kuma an umurci ma'aikata su zauna a gida.
In za a tuna hukuncin kotun koli na yin amfani da tsoffin kudi tare sa sabbi ne ya dan sauya lamura, inda gwamnatin bayan jan kafa ta mika wuya don gudun kar a ci gaba da sukar ta cewa ba ta bin umurnin kotu.
Wata matsalar ita ce ta dan karen tsada da karancin man fetur, inda farashin ke bambanta daga nan zuwa can.
Yanzu dai za a jira a ga zafin da yajin zai yi a daidai lokacin da musulmi ke shiga azumin watan Ramadan.
Ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya: