sanarwar da fadar shugaban kasar Nijer ta bayar a karshen mako ta ce shugaba Mohamed Bazoum da takwaran aikinsa Recep Tayyip Erdogan sun tattauna ta waya a kan batutuwa da dama da suka shafi tafiyar al’amura a fannoni da dama. A fannin tsaro shugabanin 2 sun cimma wata yarjejeniyar cinikayya wace a karkashinta jamhuriyar Nijer za ta yi odar jirage marasa matuka samfarin TB2 da wasu samfarin Hurkus na horon soja hade da wasu motoci masu sulke.
Wannan wani yunkuri ne da shugaban kasa ya dage akansa don ganin an kawo karshen aika aikar ‘yan bindigar da suka hana talaka walwala a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
A cewar tsohon shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasa Honorable Hama Assa, samun hadin kan kasar Turkiya don samar wa jami’an tsaro kayan aiki alheri ne ga jamhuriyar Nijer.
Abdulrahaman Alkasim, masani a sha’anin tsaro ya ce wannna na nuna cikakken ‘yancin kasar na hulda da wanda ta ke so wajen abubuwan da ta ke bukata a fannin kayan aiki, ko horo, ko musayar fasaha ko bayanai.
Wannan yarjejeniyar cinikayyar kayan yaki ta tsakanin Nijer da Turkiyya na zuwa ne a wani lokaci da al’ummar Dosso su ka fitar da sanarwar kin amincewa da shirin girke dakarun Barkhane a jihar ta Dosso mai makwabtaka da Tarayyar Najeriya da jamhuriyar Benin.
Saurari rahoton Sulei Barma cikin sauti.