Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Yiwa Masu Amfani Da Lantarki Ajin "A" Karin Kudin Wuta


Electricity pylons of high-voltage electrical power lines in Bouchain
Electricity pylons of high-voltage electrical power lines in Bouchain

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yiwa ajin "A" na masu amfani da lantarki karin kudin wuta ajin "A" shine na masu samun lantarki tsawon sa"i'o 20 a rana.

WASHINGTON DC - A yayin wani taron manema labarai a yau Laraba, Mataimakin Shugaban Hukumar Kayyade Farashin Lantarki ta Najeriya (NERC), Musliu Oseni, yace sakamakon karin yanzu kwastomomi zasu rika biyan Naira 225 akan kowace kilowat ta lantarki a sa'a guda, sabanin naira 66 da suke biya a da.

A cewar Oseni, wannan rukunin kwastomomi yana wakiltar kaso 15 cikin 100 na masu amfani da lantarki miliyan 12 a Najeriya.

Ya kara da cewar Hukumar NERC ta sauke wasu kwastomomi daga ajin "A" zuwa na "B" saboda gazawar kamfanonin samarda lantarkin na cika ka'idar yawan sa'o'in samarda wutar da ake bukata.

“A halin yanzu muna da turakun lantarki 800 da aka ware domin ajin "A", amma za'a rage su zuwa kasa da 500. Hakan na nufin cewar yanzu kaso 17 cikin 100 suka cancanci zama a turakun ajin "A". Wadannan turakun na samarda lantarki ne ga kaso 15 kacal na kwastomomin dake kansa".

Hukumar NERC ta fitar da umarni mai taken "umarnin kari na watan Afrilu" inda ta amince da samarda kilowatt 235 na lantarki a sa'a guda".

Ya kara da cewar karin kudin lantarkin ba zai shafi kwastomomin da suke sauran ajujuwa ba.

Karin kudin lantarkin ya biyo bayan sanarwar da Hukumar Kula da Kasuwancin Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta fitar a litinin din data gabata, game da karin farashin iskar gas ga kamfanonin lantarki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG