ABUJA, NAJERIYA - Karin ya nuna cewa masu sayan wuta kilowat daya kan Naira 68 yanzu za su saye shi kan Naira 225, kuma wannan kari ne da ya shafi masu samun wutar lantarki har na tsawon sa'o'i 20 a kowace rana, kuma irin wadannan su ne aka sa su a kaso na daya, wadanda ake kira Band A a turanci, sannan akwai masu kaso na biyu da ake ce masu Band B da na uku har ma da na hudu.
Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris Malagi ya yi karin haske cewa an yi kari ne kan wadanda ake ganin za su iya, wanda ya zama abu na gwaji.
Idris ya ce wadannan kudade da ake zaton za a samu daga hanun kashi 15 cikin 100 na masu samun wuta na sa'o'i 20 a kowace rana ake so a samu kudin tallafi da zai sa a ba sauran yan kasa wadanda suka kai kashi 60 wuta su ma su mora.
Kan batun azarbabi da hukumar bada wuta ta birnin tarayya Abuja wato AEDC ta yi na sayar da wuta kan sabon farashi kuma, Ministan Watsa labarai Mohammed Idris ya ce an dauki mataki na mayar wa wanda aka karbi kudin sa kan kuskure da wuta da zai sha har na tsawon lokacin da kudin sa za su kare, sannan hukumar NERC ta ci tararar kammpani AEDC tarar Naira miliyan 200.
Idris ya ce Gwamnati tana iyakacin kokarinta saboda tana kashe Naira triliyan 2.9 duk shekara wajen samar wa kasa da wutar lantarki.
Amma ga Shugaban Cibiyar kare hakkin masu amfani da wutar lantarki a Najeriya Kola Olubiyo, ya ce yawan lalacewar hanyoyin wuta a kasar ya sa yan kasa suna shan wahala, saboda haka yana kira ga shugaban kasa da ya soke sayar da hanun jarin da aka yi baki daya, saboda a sake tsari da zai samar wa kasa da wutar lantarki na din din din.
Shi ma Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai Kingsley Chinda ya fitar da sanarwa inda ya ce da shi da yanuwansa ba su amince da karin kudin wutar ba kuma zai aike wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da wasikar neman a soke karin baki daya sai abubuwa sun daidaita a kasa.
A saurari cikakkken rahoton Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna