Karancin kwararrun malamai da rashin ingantatun dakunan karatu da nisan makaranta a galibin yankunan karkara da rashin tsayayyen tsarin fasalin karantarwa da kuma rashin zuba ido akan ayyukan makarantu masu zaman kansu, na daga cikin mahimman matsalolin da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bukaci mahalarta wannan taro su yi nazari akansu don samar da mafita.
Sauran sun hada da tarnakin da matsalar tsaro ke yi wa sha’nin ilimi a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Bazoum ya ce zai kebe kashi 22 daga cikin 100 na kasafin kudaden kasa domin fannin ilimi daga shekarar 2022.
Da yake bayani a madadin shugabannin kungiyoyin malaman makarantu, sakataren kungiyar malamai ta SNEN Issouhou Arzika ya ce Mohamed Bazoum ya sosa masu inda yake masu kaikayi saboda haka sun yi na’am da manufofinsa na farfadoda harkar ilimi.
Koma bayan ilimin ‘yaya mata a Nijar ita ma wata matsala ce ta daban da ke hana ruwa gudu a kokarin ilmantar da al’ummar wannan kasa saboda haka shugaban kasa ya bayyana shirin kaddamar da wani tsarin baiwa ‘yan mata damar samun ilimi mai dorewa.
Matsalar tsaron da ta addabi jama’a a yankuna na wannan kasa ta yi sanadin rufe makarantu masu tarin yawa to amma shugaba Mohamed Bazoum ya ce ya zo da wani tsarin tattara daliban irin wadannan makarantu a cibiyoyin musamman da yake shirin kafawa domin ba su damar ci gaba da karatu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: