Gwamnatin Nijar baya ga tura sojojinta su taimaka wjen yaki da Boko Haram a kasashen Nigeria da kamaru da Cadi, ta kuma kafa dokar ta baci a jihar Diffa. A jihar ce kungiyar ta kai hari ranar litinin a kan wani gidan fursina, amma hukumomin kasar suka ce jami'an tsaro suka kore su.
Da yake magana kan dokar ta bacin da kasar ta kafa, shugaban masu rinjaye a majaisar dokokin kasar Zakari Oumarou, yace saboda irin hanyoyin da Boko Haram take bi, ta wajen amfani da yara daga yankin na Diffa, gwamnati ta baiwa jami'an tsaro dukkan iko da suke bukata domin su kare rayuka da dukiyoyin al'uma.
Mallam Zakari Oumaru yace wannan doka suna son gwanatin kasar ta fadada ta zuwa yankin Damagaram, musamman dai banagaren kasar da a tarihi take cikin daular Kanem-bornu.
Ga karin bayani