Farfasa Bube Namaiwa yace abun dake faruwa a karkashin shugabancin Goodluck Jonathan ya daure masa kai kwarai.
Maganar da shugaba Jonathan yayi, ya yita ne a matsayinsa na dan takara mai neman kuri'un 'yan Najeriya. Me yasa kafin wannan ranar bai fito ya gayawa 'yan Najeriya cewa idan an kadashi zai mika milki ga wanda ya ci zabe.
Abu na biyu me yasa tun shekarun baya bai fito kiri-kiri ya yaki 'yan ta'ada ba domin ya tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ta wallafa a duk fadin kasar sai yanzu. Magana ce ta dan siyasa domin ta fannin tsaro ya kasa.
Yau shugaba Goodluck Jonathan baya cikin shugabannin Afirka da dimokradiya ta shiga zukatansu. Duk wanda yake nazarin yanayin siyasar Najeriya haka yake hanga.Ba'a gane irin rawar da yake takawa ba ta fannin tsaro da siyasa da ma zamantakewar jama'a.
Babu abun da zai sa a yadda cewa za'a iya kwato 'yan Chibok ko shawo kan 'yan Boko Haram nan da makonni shida. Idan da yana iyawa me yasa bai yi ba tuntuni. Sabili da rikicin, mutane fiye da dubu dari suka rasa rayukansu banda asarar dukiyoyi da aka yi.Yana iyawa ya bari aka kawo wannan adadin.
Ga cikakken rahoton firar.