Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kusa a Gwamnatin Nijar ya Tabbatar da Kudurin Kasar na Yakar Boko Haram


Sojojin Nijer. (File Photo)
Sojojin Nijer. (File Photo)

Janhuriyar Nijar ta tabbatar da kudurinta na yakar kungiyar Boko Haram a ciki da ma bakotan kasashe - musamman ma Nijeriya.

Shugaban ‘yan Majalisar Dokokin Janhuriyar Nijar na jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya, Alhaji Zakari Ummaru ya tabbatar da kafa dokar ta baci a Difa ta bayar da umurni ga sojojin kasar su fafata da ‘yan Boko Haram kuma idan ma ta kama su shiga har cikin makotan kasashe su fatattake su. Da ya ke bayani ga abokin aikinmu Aliyu Mustapha, Alhaji Zakari ya ce bai ma kamata a rinka kiran mayakan ‘yan Boko Haram ba, saidai “’Yan Binku Haram,” saboda sun a fata ma Musulunci suna.

To amma ya ce a yanzu dokar umurnin yaki da Boko Haram za ta ba da dama ce ta bin Boko Haram har kan iyakar Nijeriya kodayake, a cewarsa, har akan iyakokin Nijar da Libiya da Aljeriya ana samun matsaloli kwatankwacin na Boko Haram. Ya ce lallai gwamnatin Nijar ta daura damarar yaki da Boko Haram saboda yaki da kungiyar tamkar yaki ne da makiya addinin Musulunci. Ya ce a yau dai babu wani jihadin da Musulmi zai yi wanda ya fi ya yaki Boko Haram da makamantansu.

Ya ce mahawarar sirri Majalisar dokokin Janhuriyar Nijar ta yi game da tsaro. Don haka abin da zai ce game da adadin sojojin da aka ware don tinkarar Boko Haram kawai shi ne, Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da kuma hadin gwiwar kasashen yankin tabkin Cadi sun yanke shawarar kan adadin sojojin da za a ware wato 8,700. Don haka Nijar za ta ba ta adadin da ya dace da ita na sojoji da kayan aiki. Ya tuni ma aka ware sojoji 30,000 aka girke su a jihar Difa don yaki da ‘yan Boko Haram. Bayansu ma akwai sojoji 750 da za a tura su gamayyar sojojin Kasashen masu Tafkin Cadi.

XS
SM
MD
LG