‘Yan Boko Haram sun sace wasu mutanen kasar Kamaru akalla 20 da su ka je cin kasuwa a wani kauyen da ke daura da garin Goza na Nijeriya. Wakilin Muryar Amurka a Kamaru Danda Mamadu ya kuma ce ranar Litini sojojin Kamaru sun fafata da ‘yan Boko Haram a garin Kerawa, wanda ya yi sanadin jin raunuka ga sojojin Kamaru 10 a sa’ilinda su kuma sojojin su ka hallaka ‘yan ta’addan 11 baya ga motarsu guda da su ka kama.
Hasalima ‘yan ta’addan da su ka kara da sosojin Kamarun, ‘yan leken asiri ne da kuma duba hanyoyin da su ka fi saukin bi wajen kai harin daga wani gari mai suna Warawide, inda su ka ja daga. To amma sai su ka yi kicibis da sojojin Kamarun.
Danda Mamadu, ya ce a cikin mutane 20 da ‘yan Boko Haram su ka sace din har da ‘yan mata 6. Ya ce har yanzu dai ba a san komai game da makomar matan ba. Ya ce har yanzu sojojin Kamarun na cigaba da yaki da ‘yan Boko Haram din. Ya ce ana ta shirya gangamin nuna goyon baya da kuma karfafa gwiwa ga sojojin Kamarun a yakinsu da Boko Haram.