A cewar hukumomin, wannan wani bangare ne na matakan da gwamnatin kasar ke dauka domin magance matsalar gurbata ruwa da muhalli a kasar.
Cikin wata sanarwa, shugaban cibiyar leken asiri a fadar shugaban kasa, Nii Nortey ya tabbatar da kama ‘yan kasar ta China tare da wasu ‘yan kasar Ghana biyu.
Ya ce cibiyar ta kuma yi nasarar kama makamai da wasu manyan kayan hakar ma'adinai, wato Excavators guda bakwai.
Nortey ya sake jan hankalin ‘yan kasashen waje dake zaune a Ghana da su nisanci aikata abubuwan dake sabawa dokar kasar.
Tuni wasu masu sharhi a kan harkar tsaro da hakar ma'adinai suka fara bayyana ra’ayoyinsu game da matakin da gwamnatin Ghana ke dauka a kan wanna alamari.
Musah Akambonga, tsohon babban jami'i a sashen binciken manya laifuka a Ghana ya ce matakin da gwamnati ta dauka na kama ‘yan kasar ta China ya dace kuma wannan matakin ba zai janyo tsamin dangantaka tsakanin kasashne biyu ba.
"Yawancin kamfanonin hakar ma'adinai a Ghana, mallakin mutanen kasashen waje ne tun zamanin turawan mulkin mallaka. A don haka duk wani dan China da aka kama, to wanda ba shi da takardar izini ne kuma wannan matakin ba zai janyo tsamin dangantaka tsakanin Ghana da China ba, saboda ko kasar China ba za ta amince ‘yan kasarta su rika taka doka ba, balantana ‘yan kasashen waje. A baya-bayan nan ma sai da gwamnatin Japan ta jinjinawa Ghana bisa kama wani dan Japan da ta yi bisa wasu laifukan da ake zarginsa a kasar Japan. A don haka wannan mataki ya dace", a cewar Akambonga.
Shi kuwa Baba Ahmad na kungiyar kungiyar masu hakar ma'adinai a Ghana wato Ghana National Association of Small Scale miners ya ce alakanta sashen hakar ma'adinai da siyasa shi ne abin da ke janyo cikas a kokarin da ake yi na neman shawo kan wannan matsala.
"Matsalar a wannan kasa ita ce ana alakanta sashen hakar ma'adinai da siyasa, hakan kuma ba zai taimaka ba. Mutanen China din da aka kama, za ka ji cewa an kuma sake su. Kamata ya yi gwamnati ta dauki matakin da ta dauka kan direbobi ta hanyar kafa kungiyar hakar ma'adinai karkashin gwamnati, sai a bar wa kungiyar aikin sanya ido tare da kare muhalli. In kuwa za a ci gaba da batun NPP da NDC wato jamiyyun siyasa a Ghana to ba za a samu mafita ba", a cewar Ahmad.
Ali Suraj, jami'i a fannin gudanarwa a ofishin mataimakin shugaban kasa ya ce matakin ba sani ba sabo shi ne mafi a'ala saboda hakar ma'adinai na gurbata ruwan sha da ma muhalli.
Rahoton bankin duniya mai nasaba da kare muhalli a baya-bayan nan ya ce Ghana na asarar kashi uku bisa dari na kudaden shigarta na ma’aunin GDP a kowacce shekara sakamakon gurbata ruwan sha.