Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Mahamadou Issoufou Ya Kaddamar Da Yin Hanya Daga Maradi Zuwa Najeriya


'Yan takarar shugaban kasa masu hamayya da juna Mahamadou Issoufou, a hagu, da Seini Oumarou a dama suna gaisawa
'Yan takarar shugaban kasa masu hamayya da juna Mahamadou Issoufou, a hagu, da Seini Oumarou a dama suna gaisawa

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya kaddamar da wani tsohon alkawarin aikin hanya a jihar Maradi, duk kuwa da wasu ‘yan jam’iyyun adawa na ganin ya sabawa dokar kasa da ta hana yakin neman zabe ba tare da an ce a fara a hukumance ba.

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya dasa tubulin yin wani aikin hanyar zirga-zirgar da zata dangana daga Tasawa ta Jamhuriyar Nijar har zuwa Najeriya. Da yawa sun ji dadin samun wannan aikin ci gaban da za su samu a yankinsu.

Wasu mutanen garin sun bayyanawa wakilinmu Chaibu Mani yadda suke jin dadi game da yadda suka kwashe shekaru suna neman irin wannan dama amma basu samu ba sai yau. A ganin mazauna wannan jihar ta Maradi da ke Nijar, hakan zai bunkasa kasuwanci.

Shugaba Issoufou ya fada a jawabin da ya yiwa mutanen jihar Maradi cewa, wannan cika alkawarin da ya daukarwa ‘yan Nijar din ne shekaru 5 da suka wuce. Ya kuma tabbatar musu da cewa sai inda karfinsa yak are a kan aikin matukar yana kan karagar mulkin Nijar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG