'Yan adawan da gwamnatin jamhuriyar Nijar ta cafke yanzu sun kwashe kwanaki da dama suna tsare ba tare da gurfanar dasu gaban shari'a ba.
Kawo yanzu babu wani ko dangi ko lauyoyinsu ko wasu dangi da suka san inda aka garkamesu. Har yanzu kuma gwamnatin kasar Nijar bata bayyana dalilin tsaresu ba.
Sabili da halin da wadan nan mutanen ke ciki ya sa abokansu na siyasa suka bukaci 'yan rajin kare hakin bil Adam da jakadun kasashen waje su taimaka domin nuna wa hukumomin Nijar rashin cancantar hanyoyin da suka bi suka garkame 'yan siyasan...
Tijjani Abdulkadiri jigo a kawancen 'yan adawa yace babu wata dama da gwamnati ta bada domin a sadu da mutanen. Basu bar lauyoyinsu sun gansu ba. Haka ma sun hana dangi sani inda ma ake tsare dasu. Hatta likitoci ba'a bari sun gana dasu ba.
Hukumomin shari'a da na harkokin cikin gina na kasar Nijar sun ki su ce komi illa dai wai batunsu bai kai na magana ba.
Ga karin bayani.