Da yammacin Alhamis ne kwamitin da ya kunshi jam'iyyun siyasa da wasu kungiyoyin ya gabatar da kundun rajistan masu kada kuri'u kuma dukansu suka yi amanna dashi.
Rabilu Alhaji Kani yayi magana da jam'iyyar MNSD Nasara yace hakarsu ta cimma ruwa. Tun farko sun yi korafin cewa kundun ya kunshi sunaye jabu. An bincika kuma an fitar da sunaye jabun, saboda haka sun amince. Yanzu sai 'yan kasa su je su yzabi shugabanni da Allah zai sa su zama alheri ga kasar yaddako mutum ya sha kaye zai yadda ba tare da hamayya ba..
A can baya bangaren rinjaye ya fuskanci zargi ba iyaka daga 'yan hamayya akan cewa yayi kakagida akan ayyukan fark farkon rajistan sunayen masu zaben.
Bubakar Sabo sakataren jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki yace cire sunayen mutane da dama daga kundun ba zai shafi nasararsu ba. Yace 'yan adawa ne suke korafi amma su basu da wata matsala domin su ne kan gaba a koina acikin kasar.
Ga karin bayani.