Babban darakata mai tafiyar da kungiyar wadda aka yiwa lakabi da ILJ, Alhjai Saidu Uwa, ya bayyana cewa an kafa kwamiti domin ya bi sau da kafa wajan gano wuraren da kwari masu bata amfanin gona kamar fara da sauransu suke kafin su fara gungu-gungu zuwa gonakin mutane suna barna.
Shugaban ya kara da cewa jami’an da ke kula da kwari masu barnata kayan gona ma zasu bada bayanin irin ayyukan da suka gudanar a shekarar data gabata da kuma irin shirye shiryen da suke a bana, duk kuwa da cewa akwai rahotannin cewa babu alamun farar daga inda ta saba tasowa.
A sakamakon lura da yadda tsuntsaye ke zama babbar barazana ga albarkatun gona yasa kwamitin kwararrun kungiyar gabatar da wata muhimmiyar shawara domin shawo kan lamarin, ta hanyar yiwa kwamitin garambawul.
Bankin cigaban kasashen nahiyar Afirka, mai cibiya a kasar Sudan ne ke tallafawa kwamitin da kudaden gudanar da yaki da fara, dan haka daya daga cikin wakilan da ya halarci taron ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatocin kasashen su tallafa domin kare abincin da ake samu.
Ga rahoton Sule Mumuni Barma.
Facebook Forum