Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FEMA Ta Ce Fashewar Tankar Gas Ne Sanidiyar Gobara A Ofishin Jakadancin Canada


Gobara da ta tashi a babban ofishin hukumar jakadancin kasar Kanada a Najeriya da ke Abuja, ta ci rayuka, jikkata wasu da asarar dukiyoyi
Gobara da ta tashi a babban ofishin hukumar jakadancin kasar Kanada a Najeriya da ke Abuja, ta ci rayuka, jikkata wasu da asarar dukiyoyi

Hukumar bada agajin gaggawa ta birnin Tarayya wato- FEMA ta ce fashewar wata tankar Gas ne ta janyo gobarar da ta haddasa mutuwar mutane biyu 'yan Najeriya da kuma raunata wasu karin biyu a fishin jakadancinta da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Gwamnatin kasar Canada ta ce ta gamsu ba harin ta'addanci ba ne ya yi sadiyar fashewar da ya faru a ofishin ta ba.

Cikin wata sanarwa da Ofishin Jakadancin ya fitar dazu dazunnan a Abuja, yace kawo yanzu bisa bayanan da ake da shi a hannu, ana iya cewa gobara ce ta jawo fashewar ba wani aikin ta'addanci ba.

''Muna tabbatar da cewa dukkannin ma'aikatan ofishin jakadancinmu da ke Abuja suna nan lafiya, ba wanda ya sami rauni, kuma muna aiki da hukumomin Najeriya don gano ainihin abinda ya faru. Za a gudanar da bincike amma dai a halin yanzu, muna ganin hatsari ne kawai ya faru'' a cewar sanarwar.

Biyo bayan wannan fashewa dai, ofishin jakadancin na Canada ya dakatar da ayyukansa har zuwa wani lokaci tukun.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawar, Nkechi Isa cikin sanarwar da ta sanyawa hanu, ta ce fashewar ta kuma kone wani sashi na ofishin jakadancin.

Da misalin karfe goma da minti arba'in da biyar na safiyar Litinin dinnan ne lokacin da ake gyara Janarta samfurin MIKANO. "A daidai lokacin da janeraten ke aiki, wata motar tanki mai dauke da litar GAS dubu biyu ta yi wani fashewa abin kenan da ya haddasa gobarar'' a cewar sanarwar.

Tuni dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mika sakon jaje ga gwamnatin kasar Canada, da kuma ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalan wadanda su ka rasa rayukansu, ya na mai bayyana hakan a matsayin babban abin bakin ciki.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG