Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 15 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kasar Canada


Hayaki Na Fitowa Daga Hatsarin Mota Da Ya Kashe Mutane 15 a Carberry, da ke Yammacin Winnipeg, Canada. June 15, 2023.
Hayaki Na Fitowa Daga Hatsarin Mota Da Ya Kashe Mutane 15 a Carberry, da ke Yammacin Winnipeg, Canada. June 15, 2023.

Jami’ai a kasar Canada sun ce akalla mutane 15 su ka mutu a ranar Alhamis a lokacin da wata babbar motar daukar kaya ta yi karo da wata karamar motar safa da ke dauke da wasu mutane, galibi dattawa, a kan hanyarsu ta zuwa gidan caca a lardin Monitoba na kasar Canada.

Mataimakin kwamishinan rundunar ‘yan sandan kasar a lardin Monitoba, Rob Hill, ya ce akwai mutane kusan 25 a cikin motar.

Hukumomi sun ce an kwantar da mutane goma a asibiti.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya bayar da rahoton cewa, direbobin motocin biyu sun tsira daga hatsarin kuma suna kwance a asibiti.

“Labarin da hatsarin da aka samu daga garin Carberry a lardin Manitoba abu ne mai tada hankali matuka,” abin da Firai Ministan Canada Justin Trudeau ya wallafa a shafinsa na twitter kenan.

Ya kara da cewa “a yau ina mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, haka kuma ina jajanta wa wadanda suka samu raunuka. Ba zan iya kwatanta bakin cikin da wadanda abun ya shafa ke ji ba, amma al'umar Canada na tare da ku.”

XS
SM
MD
LG