Hukumar yaki da fatauci da miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta shiga sabuwar shekarar 2025 tare da nasarar kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi a sassan daban-daban na kasar, cikin su har da wani mai shirya fina-finai a masana’antar Nollywood da ya sami horo a kasar Amurka da kuma wata shahararriyar shugabar masu safarar kwayoyi a birnin Ikko.
Cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, jami’an hukumar sun kama Emeka Emmanuel Mbadiwe, wani mai shirya fina-finai kuma mai jawaban hikima (motivational speaker) a ranar 27 ga watan Disamban bara, a wani otel a yankin Lekki da ke birnin Legas.
Sanarwar ta ce nasarar kama Mbadiwe ta biyo bayan tsare wani abokin huldar sa Uzoekwe Ugochukwu James a wani gidan ajiya da ke rukunin gidajen Ajao a Ikeja.
Dubun james ta cika ne sa’adda ya ke kokarin karbar kunshin "LOUD 33," wani nau’in tabar wiwi mai nauyin kilogram 17.30, bayan da kayan suka isa bangaren kasa-da-kasa na filin jirgin saman Murtala Muhammed, daga wani jirgi da ya taso daga Amurka a ranar 24 ga watan Disamban bara cikin wasu akwatunan katako.
Haka nan kuma hukumar ta yi nasarar cafke shahararriyar mai safarar kwayoyi a Legas din, Alhaja Aishat Feyisara Ajoke Elediye mai shekaru 61, wace ake mata inkiya da “Iya Ruka”, a gidan ta da ke yankin Okota.
Alhaja ta shiga hannu ne bayan da aka kama wata babbar motar daukan kaya makare da tabar wiwi da yawan ta ya kai kilogram 1,540.
Duka da cewa ta kasance shaharariyar mai sai da tufafi daga kasashen waje, bincike ya nuna cewa, ta na jagorar gugun masu sai da kwayoyi a yankin Mushin na birnin Ikko.
A ranar 29 ga watan Disamban 2024 kuma, yayin wani samame a gidajen su, hukumar NDLEA a jihar Kwara ta yi nasarar kama Khadjat Abdulraheem mai shekaru 24 da Ayomide Morakinyo mai shekaru 20 da laifin sai da cake mai kumshe da kwaya a ciki.
Sanarwar ta Babafemi ta kara da cewa, ta sake kama wani mai suna Sodade Sunday Eniola, wani da ya taba fadawa komar hukuma da laifin safarar fasfo.
Laifin da ya sa aka kama shi a baya ya shafi safarar kwayoyi wanda ya biya tarar kudi a madadin zaman gidan kaso.
Dandalin Mu Tattauna