Wata kungiyar sa kai da hadakar ‘yan tawaye sun zargi sojojin Mali da sojojin hayar Rasha da alhakin kaiwa fararen hula cikin wata mota hari, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum 9 da suka hada da mata da yara a yankin Segou a kasar Mali a makon jiya.
Motar wace ta taso daga garin Niono ta nufi wani sansanin ‘yan gudun hijira dake Mauritania a ranar Alkhamis a sa’adda aka bude mata wuta, a cewar Mohamed Elmaouloud Ramadane, khakakin kungiyar hadakar 'yan tawayen Tuareg dake neman ‘yancin cin gashin kansu a Arewacin Mali.
Muhamed da kungiyar ta sa kan al’ummar ta Kel Ansar sun ce dakarun Mali da mayakan Rasha na Wagner ne suka kai harin.
Cikin wata sanarwa ta daban, shugaban Kel Ansar, daya daga cikin kungiyoyin Tuareg mafi girma, ya bukaci a gudanar da bincike, to sai dai, dakarun Mali, sun ce babu hannun su a wannan zubar da jinni.
Hukumomin sojin Mali basu mai da martini kan sakon da aka aike musu don neman jin ta bakin su ba.
An kasa tuntubar mayakan Wagner nan take.
Tun bayan juyin Mulki 2 da akayi a 2020 da 2021 wanda sojoji suka karbe ikon gwamnati a Mali, sannan suka kore Faransa da dakarun MDD a kasar, mayakan Wagner suke Mali. Inda suke tallafawa dakarun Mali a yakin da suke yi da masu tsatsaurar ra’ayin Islama da ‘yan tawayen Tuareg.
A wata Dizamban bara, kungiyar kare hakkin bil- Adama na Human Rights Watch, ta ce dakarun Mali, wadanda mayakan Wagner da kungiyoyin Islama masu daukan makamai sun aikata laifukan take hakkin bil- Adama ga fararen hula wadanda suka sabawa dokokin yaki.
Dandalin Mu Tattauna