Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Faransa Sarkozy Zai Fuskanci shari’a Mai Alaka Da Karban Na Goro Daga Ghaddafi

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da kasarsa ke wa Carlos The Jackal Shari'a
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da kasarsa ke wa Carlos The Jackal Shari'a

Yawan shari’un da Sarkozy yake fuskanta sun dishashe shekarun da ya kwashe yana aiki tun bayan da ya fadi zabe a 2012. Sai dai kuma har yanzu ya ci gaba da kasancewa madubin duba ga mutane da dama sannan sanin kowa ne cewa yana yawan ganawa da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a kai akai.

Yau Litinin, tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, wanda aka same shi da laifi sau 2 a wasu mabanbantan shari’u tun bayan da ya sauka daga karagar mulki wanda ke da alaka da karbar kudade ta hanyar da basu dace ba don gudanar da gangamin zabe a wata yarjejeniya da tsohon shugaban Libya marigayi Maumar Ghadafi.

Yawan shari’un da Sarkozy yake fuskanta sun dishashe shekarun da ya kwashe yana aiki tun bayan da ya fadi zabe a 2012. Sai dai kuma har yanzu ya ci gaba da kasancewa madubin duba ga mutane da dama sannan sanin kowa ne cewa yana yawan ganawa da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a kai akai.

An sami gogagen dan siyasa, mai shekaru 69 a duniya wanda ya kasance mijin mai talla sannan mawakiyar nan Carla Bruni, kana, a lokacin da yake rike da ikon kasar tsakani 2007 zuwa 2012 yana sha’awar da a kira shi da Hyper-President da laifi a wasu shari’u guda 2, wanda aka sake samun shi da wani laifin sannan ana binciken shi akan wasu shari’u guda 2.

Sarkozy zai bayyana gaban kuliya a wata kotu a Paris kasa da rabin wata bayan da wata babar kotun daukaka kara a kasar ta Faransa ta yi fatali da daukaka karar da yayi akan wani hukuncin da aka yanke mishi zaman gidan kaso tsawon shekara guda bisa samun shi da laifin yin amfani da ikon shi don cimma wata manufa wanda aka amince a sanya mishi na’urar GPS a kafan sa a madadin zaman gidan kaso.

Shari’ar bayan nan da yake fuskanta, ta kasance sakamakon binciken da aka gudanar tsawon shekaru 10 kan zargin da ake yiwa Sarkozy da karbar na goro don taimakawa Ghaddafi a gangamin yakin neman zaben da ya kai shi ga samun nasara a zaben 2007 da rahotanni suka bayyana cewa kudaden sun tasamma euro miliyan 50.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG