Costas Simitis, tsohon firai ministan Girka kuma wanda ya tsara tsarin shigar kasar cikin kudin bai daya na Turai, wato Euro, ya mutu yana da shekaru 88, kamar yadda gidan talabijin na kasar TV ERT ya rawaito.
Kafafen yada labaran Girka sun nakalto daraktan asibitin birnin Corinth na cewa, an kawo Simitis asibitin ne da sanyin safiya ranar Lahadi daga gidansa na hutu a yammacin birnin Athens, a sume kuma baya numfashi. Za’a kuma gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar sa.
Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki hudu a hukumance. Za’a yi wa Simitis jana’izar girmamawa ta kasa.
Wanda ya kafa jam’iyyar PASOK mai ra’ayin gurguzu a shekarar 1974, ya zama shugaban masu kawo sauyi na jam’iyyar, inda suka fafata da shugaban jam’iyyar Andreas Papandreou kafin daga bisani ya gaje shi a shekarar 1996.
Shugabancin sa, wanda ya kasance daga watan Janairun 1996 zuwa watan Maris na 2004, har yanzu yana rike da tarihin gwamnatin Girka da ta fi dadewa.
Baya ga shigar kasar cikin kasashen Turai, a shekarar 2001, a wa’adin mulkin sa ya yi nasarar takarar karbar bakunci wasanni Olympics na 2004, wani babban shiri na gina ababen more rayuwa da kuma taimakawa Cyprus shiga kunigyar EU a 2004.
Dandalin Mu Tattauna